Sabon Fira Ministan Guinea Conakry Ya Sanar Da Sunayen Sabbin Ministocinsa
Sabon fira ministan kasar Guinea Conakry ya sanar da sunayen sabbin ministocinsa tare da barin wasu tsoffin ministocin a kan mukamansu.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya watsa rahoton cewa: A wata sanarwa da sabon fira ministan kasar Guinea Conakry ya fitar a cikin daren Asabar: Ibrahim Kassory Fofana ya bayyana sunayen mutane 33 a matsayin sabbin ministocinsa duk da cewa tsoffin ministocin tsaro, harkokin waje, shari'a da na harkokin gudanar da jihohi ya bar su a kan mukamansu na baya.
A ranar Litinin 21 ga wannan wata na Mayu ne shugaban kasar Guinea Conakry Alpha Conde ya sanar da Ibrahim Kassory Fofana a matsayin sabon fira ministan kasar a kokarin da yake yi na ganin ya shawo kan rikicin siyasar da ya kunno kai a kasar sakamakon zargin da 'yan adawar kasar ke yi cewa yana son yin tazarce a zaben shekara ta 2020.
Kafin nadin nasa a matsayin sabon fira ministan Guinea Ibrahim Fofana shi ne ministan ma'aikatar zuba hannun jari ta kasar a tsohuwar gwamnatin fira minista Mamady Youla da ta yi murabus a makon da ya gabata..