An Hallaka Babban Kwamandan Kawancen Saudiya A Yemen
Majiyar tsaron hadaddiyar daular larabawa ta sanar da cewa an hallaka babban kwamandan rundunar kawancen saudiya a gabar tekun yammacin kasar Yemen
Tashar talabijin din Al-alam ta nakalto majiyar tsaron hadaddiyar daular larabawa na cewa a daren jiya talata, babban kwamandar rundunar kawancen saudiya ya hallaka sanadiyar harin da dakarun tsaron Yemen suka kai da makami mai linzami a gabar ruwan yammacin kasar.
A bangare guda, majiyar tsaron yemen ta sanar da hallaka da jikkata sojojin hayar saudiya da dama a gabar ruwan yammacin kasar tare da tarwatsa wasu motoci yakinsu sama da 20 da kuma kame wasu 10 daga cikinsu.
Har ila yau Sojoji da dakarun sa kai na yemen sun katse hanyoyin kai dauki na sojojin hayar saudiyar a hanyoyin Annahila da Mujailis a gabar ruwan yammacin kasar, sannan kuma sun hallaka sojojin hayar saudiyan da dama a Duraihami da kuma tarwatsa kayan yakinsu, lamarin da ya sanya wasunsu da dama suka gudu.
A gafe guda kuma majiyar tsaron yemen din ta sanar da dakile harin sojojin saudiya a yankunan Jabalul-Sha'ir da yammacin Majazah a jahar Asir na kasar Saudiya, inda suka hallaka tare da jikkata wasu da dama daga cikinsu.