Sojojin Yemen Sun Harba Makamai Masu Linzami Akan Babban Birnin Saudiyya
A daren jiya ne sojojin kasar ta Yemen su ka kai wa birnin Riyadh hari
Kamfanin dillancin labarun reuters ya ce; An ji karar fashewar wasu abubuwa masu karfi da kuma ganin hasken wuta a saman birnin Riyadh.
A can kasar Yemen sojojin kasar sun sanar da harba makamai masu linzami samfurin "Burkan H 2" akan ma'aikatar tsaron Saudiyya da kuma wasu cibiyoyin gwamnatin kasar a cikin birnin Riyadh.
Kakakin sojan Yeman Sharaf Lukman ya jaddada cewa; Za su ci gaba da kai hare-hare da makamai masu linzami akan cibiyoyin tattalin arziki na Saudiyya matukar Saudiyyar ba ta daina kai wa kasar Yemen hari ba.
Tun a cikin watan Maris na 2015 ne dai Saudiyyar take jagorantar kawancen yaki da kasar Yemen, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane fiye da 12.000.