Yemen: An Kashe Sojojin Saudiyya Masu Yawa Akan Iyaka
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32072-yemen_an_kashe_sojojin_saudiyya_masu_yawa_akan_iyaka
Tashar talabijin din al-Masirah ta kasar Yemen ta ba da labarin cewa; maharba sojojin kasar ta Yemen sun halaka sojojin Saudiyya biyu a sansanin al-dud.
(last modified 2018-08-22T07:02:01+00:00 )
Jun 27, 2018 02:47 UTC
  • Yemen: An Kashe Sojojin Saudiyya Masu Yawa Akan Iyaka

Tashar talabijin din al-Masirah ta kasar Yemen ta ba da labarin cewa; maharba sojojin kasar ta Yemen sun halaka sojojin Saudiyya biyu a sansanin al-dud.

 Rahoton talabijin din ya ci gaba da cewa; Sojojin na Yemen sun kuma harbo wani sojan Saudiyyar guda da kuma da sansanin soja na al-Rumaih a gundumar jizan da ke kudancin Saudiyya.

A wani gefen, dakarun sa-kai na Ansarullah sun kashe 'yan koren Saudiyya masu yawa a yankin al-Riyah da ke kusa da babban birnin kasar Sanaa.

Kasar Saudiyya wacce take samun cikakken goyon bayan Amurka ta shelanta yaki akan kasar Yemen a watan Maris na 2015 wanda kawo ya zuwa yanzu an kashe fiye da mutane 12,000 da jikkawa wasu dubbai.