Tashin Bam Ya Hallaka Mutun Guda A Arewa Maso Yammacin Bagdaza
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32195-tashin_bam_ya_hallaka_mutun_guda_a_arewa_maso_yammacin_bagdaza
Kafafen Sadarwar Iraki sun sanar da tashin wasu tagwayen bama-bamai a yankin Ashu'ula dake arewa maso yammacin birnin Bagdaza babban birnin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:02:04+00:00 )
Jul 05, 2018 02:12 UTC
  • Tashin Bam Ya Hallaka Mutun Guda A Arewa Maso Yammacin Bagdaza

Kafafen Sadarwar Iraki sun sanar da tashin wasu tagwayen bama-bamai a yankin Ashu'ula dake arewa maso yammacin birnin Bagdaza babban birnin kasar.

Sanarwar ta ce lamarin ya auku ne a jijjifin safiyar wannan alhamis, inda ya zuwa yanzu aka tabbatar da mutuwar mutum guda tare da jikkatar wasu 11 na daban.

Duk da cewa an samu nasara kan kungiyar ta'addanci nan ta ISIS a Iraki, amma har yanzu akwai 'ya'yan wannan kungiyar a yankunan daban daban na cikin kasar inda suka kaddamar da ayyukan ta'addanci.

A shekarar 2014 ne kungiyar ta'addancin nan ISIS bisa cikekken goyon bayan Amurka da kawayenta na yamma da larabawa daga cikinsu kasar Saudiya suka mamaye wani bangare mai fadi na arewa da yammacin kasar ta Iraki, inda suka aikata ta'addancin da babu irinsa, to saidai kasar ta Iraki ta bukaci makwabciyarta wato Iran da ta taimaka mata wajen yakar wadannan ta'adda.

A ranar juma'a 17 ga watan Nuwambar 2017 Dakarun kasar Iraki da na sa kai tare da mashawartar sojoji na jamhoriyar musulinci ta Iran sun samu nasarar tsarkaka garin Rawa da ya karshen tungar 'yan ta'addar ta ISIS a Iraki.