Wani Matashin Bapalastine Ya Yi Shahada A Zirin Gaza
Wani Matashin Bapalastine da ya jikkata sanadiyar harbin da sojojin sahayuwa suka yi masa ya yi shahada a jiya Laraba.
Kakakin ma'aikatar kiyon lafiya ta Palastinu Asharaf Kudrat ya sanar da cewa wani matashi mai shekaru 16 a Duniya da Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka harbe sa a ranar 14 ga watan Mayun da ya gabata a gabashin zirin Gaza ya yi shahada a jiya Laraba.
A cikin makonin baya-bayan nan Al'ummar Palastinu sun gudanar da zanga-zangar nemo dawo da hakki, wannan zanga- zangar lumana da aka fara tun daga ranar 30 ga watan Maris din da ya gabata wato ranar kasa har yanzu ana ci gaba da ita a yankin na Zirin Gaza.
Daga ranar 30 ga watan Maris zuwa yanzu Palastinawa 144 ne suka yi shahada sanadiyar buda musu wuta da jami'an tsaron HKI suke yi , daga cikinsu akwai kananen yara 17, sannan kuma akwai wasu sama da 15000 da suka jikkata.
Da dama daga cikin kasashen Duniya masu 'yanci cikin har da jamhoriyar musulinci ta Iran sun yi alawadai da wannan ta'addanci.