Syria: Wani Kwamandan "Yan Ta'adda Ya Mika Kai Ga Sojojin Gwamnati
Majiyar tsaron kasar Syria ta ce wani daga cikin kwamandojin kungiyar Syrian Free Army mai suna Adham al-Akrad, ya mika kansa ga sojojin kasar a yankin Dar'aa.
Majiyar ta ci gaba da cewa Adham al-Akrad ya kuma mika makaman da suke a karkashinsa da rundunarsa.
A gefe daya kungiyar kare hakkin dan adam ta : "Human Right Watch" ta ambato majiyar 'yan ta'adda ta babbatar da cewa sojojin kasar ta Syria sun shimfida ikonsu a yankuna masu fadi na Dar'aa. A cikin kwanaki 18 da suka gabata ne sojojin Syria suka kashe 'yan ta'adda 131 a cikin yankin na Dar'aa.
A karshen watan Yuni ne dai sojojin na Syria suka bude kai farmaki akan tungar 'yan ta'addar kungiyar; Syrian Free Army' a yankin Dar'aa da ke kan iyaka da kasar Jordan. Kawo ya zuwa yanzu kaso 90% na gundumar Dar'aa ta koma karkashin ikon gwamnatin Syria, bayan da aka fatattaki 'yan ta'adda daga ciki.