Yemen: An Kashe Sojojin Saudiyya 4 Akan Iyaka
Jul 16, 2018 02:21 UTC
Sojojin Saudiyyar 4 ne su ka halaka a wani taho mu gama da sojojin kasar Yemen
Bugu da kari sojoji da dakarun sa-kai na kasar Yemen sun sami nasarar kwace iko da wasu kauyuka hudu a cikin gundumar Jizan ta Saudiyya.
Majiyar sojan Yemen ta ce; Sun kuma kame sojojin Saudiyya masu yawa a matsayin fursunonin yaki a harin da su ka kai a jizan
Kasar Saudiyya ta fara kai wa Yemen hari ne tun a watan Maris na 2015 bisa cikakken goyon bayan kasar Amurka. Kawo ya zuwa yanzu dai fiye da mutane 12000 ne hare-haren na Saudiyya su ka kashe a Yemen. Wasu dubban dubatar kuma su ka jikkata. Har ila yau sojojin na Saudiyya sun lalata cibiyoyin kiwon lafiya da asibitoci masu yawa.