Dakarun Tsaron Yemen Sun Halba Makami Mai Linzami Cikin Kasar Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32379-dakarun_tsaron_yemen_sun_halba_makami_mai_linzami_cikin_kasar_saudiya
A matsayin mayar da martani kan irin ruwan bama-baman da jiragen yakin kawancen Saudiya ke yi a kasar, Dakarun tsaron yemen sun halba makami mai linzami zuwa birnin Najran na kasar Saudiya
(last modified 2018-08-22T07:02:07+00:00 )
Jul 18, 2018 13:44 UTC
  • Dakarun Tsaron Yemen Sun Halba Makami Mai Linzami Cikin Kasar Saudiya

A matsayin mayar da martani kan irin ruwan bama-baman da jiragen yakin kawancen Saudiya ke yi a kasar, Dakarun tsaron yemen sun halba makami mai linzami zuwa birnin Najran na kasar Saudiya

Kamfanin dillancin Labaran Annashra ya nakalto Dakarun tsaron kasar ta yemen na cewa sun halba makami mai linzami zuwa sansanin sojojin Saudiya na jihar Najran dake kan iyaka da kasar a matsayin mayar da martani kan hare-haren da jiragen yakin kawancen Saudiyar ke kaiwa cikin kasar su.

Saidai kafafen yada Labaran saudiyar sun yi da'awar cewa makaman kariya na kasar sun kakkabo makamai masu Linzamin da Sojojin yemen din suka halba cikin kasar.

A Daren litinin din da ta gabata ma, sojoji tare da dakarun sa kai na kasar yemen din sun halba makamai masu  linzami a wuraren taruwar sojojin hayar saudiya a gabar ruwan yammacin kasar.

A bangare guda, Shugabanin  kabilu da na jihar Alhudaida sun yi wani  zama na musaman, inda a cikin zaman suka yi watsi da mamayar da ake kokarin yiwa jihar ta su, sannan sun jadadda goyon bayansu na kare gabar ruwan yammacin kasar daga mamaya tare kuma da meka godiya ta musaman ga Sayyid Hasan Nasrullah shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labnon kan goyon bayan da yake bayarwa ga Al'ummar Yemen da kuma Abdulmalik Alhutsi , shugaban kungiyar Ansarullah na kasar dangane da jajircewar da ya yi wajen kare kasar daga mamayar Saudiya da kasashen Amurka gami da na Turai.