Palastinawa 3 Sun Yi Shahada A yayin Zanga-zangar Zirin Gaza
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32405-palastinawa_3_sun_yi_shahada_a_yayin_zanga_zangar_zirin_gaza
Dakarun HK Isra'ila sun bindige Palastinawa 3 har lahira a yayin zanga-zangar da suke gudanar na neman a dawo musu da hakinsu a wannan juma'a
(last modified 2018-08-22T07:02:08+00:00 )
Jul 20, 2018 13:39 UTC
  • Palastinawa 3 Sun Yi Shahada A yayin Zanga-zangar Zirin Gaza

Dakarun HK Isra'ila sun bindige Palastinawa 3 har lahira a yayin zanga-zangar da suke gudanar na neman a dawo musu da hakinsu a wannan juma'a

Cibiyar sadarwar Palastinu ta sanar da cewa a yayin da aka shiga juma'a ta 17 na zanga-zangar neman dawo da hakki, al'ummar yankin Zirin Gaza sun gudanar da zanga-zangar a wannan juma'a tare da rera taken makircin Isra'ila bai ci nasara ba na take hakin 'yan gudun hijrar Palastinu, jami'an tsaron HK Isra'ila dake cikin halin ko ta kwana a gabashin yankin Khan Yunus sun buda wuta ga mahalarta zanga-zangar.

A bangare guda kuma, Dakarun Isra'ilan sun kai hari kan cibiyoyin kungiyar gwagwarmaya na Palastinawan a gabashin asansanin Al-barij dake tsakiyar zirin Gaza da kuma gabashin Khan Yunus tare da kashe Mutun uku da jikkata wasu da dama na daban.

A bangare guda, jaridar Sahayuna ta habarta cewa an yi musayar tsakanin mayakan gwagwarmaya da Sojojin Isra'ila a kan iyakan zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar wani Sojin Isra'ila guda.

Daga lokacin da Palastinawa suka fara zanga-zangar lumana na neman a dawo musu da hakinsu a ranar 30 ga watan Maris zuwa yanzu, Palastinawa 149 ne suka yi shahada a hanun Dakarun HK Isra'ila sannan kuma sama da dubu 16 ne  suka jikkata.