Dakarun Kasar Iraki Sun Shiga Birnin Hait Da Ke Lardin Anbar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i3241-dakarun_kasar_iraki_sun_shiga_birnin_hait_da_ke_lardin_anbar
Sojojin gwamnatin Iraki tare da mayakan sa kai sun shiga birnin Hait daga ke cikin Lardin Anbar a daren jiya.
(last modified 2018-08-22T06:58:04+00:00 )
Apr 01, 2016 05:10 UTC
  • Dakarun Kasar Iraki Sun Shiga Birnin Hait Da Ke Lardin Anbar

Sojojin gwamnatin Iraki tare da mayakan sa kai sun shiga birnin Hait daga ke cikin Lardin Anbar a daren jiya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, sojojin kasar tare da mayakan sa kai na kasar sun samu nasarar fattatakar 'yan ta'addan ISIS da ke rike da birnin na Hait kusan shekaru biyu.

Brigadier General Abdullah Ubaidi babban jami'in soji da ke jagorantar farmaki kan 'yan ta'adda a Lardin Anbar ya fadi daren jiya cewa, wannan yana daga cikin shirinsu da suka fara aiwatarwa, na tsarkake dukaknin yankunan arewacin kasar Iraki da ke hannun 'yan ta'addan Daesh.