Sojojin Siriya Sun Tsarkake Kashi 98% Na Jihar Dar'a
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32513-sojojin_siriya_sun_tsarkake_kashi_98_na_jihar_dar'a
Masu rajin kare hakin bil-adama na bangaren 'yan adawa sun sanar a wannan assabar cewa Sojoji da dakarun sa kai na kasar sun mamaye kashi 98% na jihar Dar'a na kudancin kasar
(last modified 2018-08-22T07:02:10+00:00 )
Jul 28, 2018 08:18 UTC
  • Sojojin Siriya Sun Tsarkake Kashi 98% Na Jihar Dar'a

Masu rajin kare hakin bil-adama na bangaren 'yan adawa sun sanar a wannan assabar cewa Sojoji da dakarun sa kai na kasar sun mamaye kashi 98% na jihar Dar'a na kudancin kasar

A ranar 13 ga watan yuli ne Sojojin siriya da Dakarun sa kai suka sanar da cewa sun samu nasarar tsarkake garin Dar'a na tsakiyar jihar Dar'a.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto masu rajin kare hakin bil-adama na kasar Siriya na ishara kan ci gaban da sojoji ke yi a yankin Haudu-Yarmuk dake arewa maso yammacin Dar'a na cewa, a halin da ake ciki kashi biyu kacal ya rage na jihar Dar'a a hanun 'yan ta'adda.

har ila yau a ci gaba da tsarkake yankunan da aka fatattaki 'yan ta'adda daga cikinsu, Sojoji da dakarun sa kai na Siriyan sun gano wani wuri na Dakarun MDD a kauyen Sahami-Gullan dake gefen arewa maso yammacin garin na Dar'a, da aka cikinsa aka gano nakiyoyi da kayayyaki yaki masu yawa.