An Fallasa Harkar Kasuwanci Tsakanin Kasar Morocco Da HKI
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32517-an_fallasa_harkar_kasuwanci_tsakanin_kasar_morocco_da_hki
Kafafen yada labarai na kasar Morocco sun fallasa dangantakar kasar ta kasuwanci da haramtacciyar kasar Israela.
(last modified 2018-08-22T07:02:10+00:00 )
Jul 28, 2018 14:36 UTC
  • An Fallasa Harkar Kasuwanci Tsakanin Kasar Morocco Da HKI

Kafafen yada labarai na kasar Morocco sun fallasa dangantakar kasar ta kasuwanci da haramtacciyar kasar Israela.

Wani shafin labarai na yanar gizo ya bayyana cewa duk kokarinda jami'an gwamnatin kasar suka yi ta yi a baya na musanta cewa akwai dangantakar tsaro ko kuma ta kasuwannin tsakanin kasar da HKI ya tabbata ba gaskiya ba ne. Don abinda ya fito a fili shi ne cewa gwamnatin kasar Morocco ta dade tana dangantakar tsaro da kasuwanci da HKI kuma har yanzun tana mutunta wannan dangan takar.

Shafin yanar gizon ta kara da cewa Kakakiin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Morocco Mustafa Al-khalafi ya sha bayyana cewa babu wata dangantaka tsakanin gwamnatin kasar da Haramtacciyar kasar Israela, amma jaridan HKI a ranar laraba da ta gabata sun fallasa a irin dangantakar kasuwanci da tsaron da  HKI take da su da kasashen larabawa daga ciki har da kasar Morocco. 

Wani shafin yanadar gizo na labarai masu suna "Al-Umqul Magribi " ya ce bisa rahoton cibiyar bincike na Al-Zaytuna kasar morocco ita ce na biyar a cikin kasashen larabawa 10 wadanda suke harkar kasuwanci da HKI, kuma yawan kudaden da da suke musayar kasuwanci a tsakaninsu ya kai dakar Amurka billiyon 48.