Isra'ila Ta Kai Hari Yankin Zirin Gaza
Majiyar Palastinu ta sanar da cewa a safiyar wannan lahadi, HK Isra'ila ta kai hari da jirgi masar matuki kan wasu gungun matasan Palastinawa a yankin zirin Gaza.
Sojojin Isra'ilan sun yi da'awar cewa matasan na kokarin tura jirgin balam-balam mai dauke da wuta zuwa kauyukan yahudawa 'yan kama wuri zauna.
Ya zuwa yanzu ba a bayyana irin asarar da wannan hari ya janyo ba.
Aikewa da jiragen leda da na balam balam dauke da wuta zuwa yankuna yahudawa 'yan kama wuri zauna na a matsayin wata gwagwarmaya da Palastinawa suka billo da ita wajen tunkarar Sahayuna.
Tun daga ranar 30 ga watan Maris zuwa yanzu ana ci gaba da zang-zangar lumana na neman dawo da hakki, a yankin zirin Gaza, kuma ya zuwa yanzu, sama da Palastinwa 150 ne suka yi shahada yayin da wasu sama da dubu 16 na daban suka jikkata, sanadiyar buda wuta da sojojin sahayuna suka yi musu a lokacin zanga-zangar.