Kungiyar (IS) Ta Sace Mata Da Yara 36 A Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32551-kungiyar_(is)_ta_sace_mata_da_yara_36_a_siriya
Bayanai dag Siriya na cewa kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ta sace mata da yara a kalla 36 bayan mummunan harin data kai a makon da ya gabata a lardin Suweda.
(last modified 2018-08-22T07:02:10+00:00 )
Jul 30, 2018 09:43 UTC
  • Kungiyar (IS) Ta Sace Mata Da Yara 36 A Siriya

Bayanai dag Siriya na cewa kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ta sace mata da yara a kalla 36 bayan mummunan harin data kai a makon da ya gabata a lardin Suweda.

Kungiyar dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama ta OSDH a Siriyar, ta sanar da cewa mata da yaran 'yan kabilar Druze an yi garkuwa dasu ne a yayin farmakin da kungiyar mayakan dake ikirari da sunan jihadi ta IS ta kai a lardin a ranar 25 ga watan Yulin nan, inda mutane sama da 250 suka rasa rayukansu.

Wadanda akayi garkuwa da su sun hada da mata 20 da kuma yara 16 a cewar kungiyar ta OSDH da kuma wani shafin intaner Sueda24. 

Kungiyar dai ta IS bata fitar da wani bayyani ba kan wanann labarin.

Harin da kungiyar ta IS ta dauki alhakin kai wa a lardin na Sueda a baya bayan nan, shi ne irinsa mafi muni, tun bayan da kasar ta Siriya ta tsuduma cikin yaki a shekara 2011.