Yemen : Harin Saudiya Ya Kashe Mutum 52 A Hudaida
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32599-yemen_harin_saudiya_ya_kashe_mutum_52_a_hudaida
Majiyar Yemen ta sanar a daren jiya alhamis cewa adadin mutanan da suka rasa rayukansu sanadiyar harin ta'addancin da jiragen yakin kawancen saudiya suka kai asibitin al-thaurah da ke garin al-Hudaidah dake arewacin kasar ya haura zuwa 52.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 03, 2018 02:16 UTC
  •  Yemen : Harin Saudiya Ya Kashe Mutum 52 A Hudaida

Majiyar Yemen ta sanar a daren jiya alhamis cewa adadin mutanan da suka rasa rayukansu sanadiyar harin ta'addancin da jiragen yakin kawancen saudiya suka kai asibitin al-thaurah da ke garin al-Hudaidah dake arewacin kasar ya haura zuwa 52.

Har ila yau majiyar ta ce adadin wadanda suka jikkata ya haura zuwa 70.

Kafin hakan dai majiyar kasar Yemen din ta bayyana cewa Bayan harin da jiragen yakin kawancen Saudiyya su ka kai akan asibitin, sun kuma kai wasu hare-haren a cikin unguwannin birnin wanda kawo ya zuwa yanzu mutane 26 ne su ka yi shahada yayin da wasu 35 suka jikkata.

Kungiyar Hutsi na kasar Yemen din ta bayyana harin da laifin yaki, yayin da tashar talabijin din al-Mayadeen da ke Lebanon ta bayyana abin da ya faru da kisan kiyashi.

Saudiyya ta tsananta kai hare-hare akan fararen hular kasar Yemen a cikin kwanakin nan, saboda rufe kashin da suke sha a hannun sojoji da dakarun sa-kai na Kasar.