Palasdinu: Kungiyar Hamas Ta Sha Alwashin Mayar Wa Da HKI Martani
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32675-palasdinu_kungiyar_hamas_ta_sha_alwashin_mayar_wa_da_hki_martani
Reshen sojan kungiyar Hamas ta Palasdinu, izzuddin al'qassam ya ce zai mayar da martani akan kisan mayakansa biyu da sojojin HKK su ka yi
(last modified 2019-03-18T02:12:56+00:00 )
Aug 08, 2018 03:04 UTC
  • Palasdinu: Kungiyar Hamas Ta Sha Alwashin Mayar Wa Da HKI Martani

Reshen sojan kungiyar Hamas ta Palasdinu, izzuddin al'qassam ya ce zai mayar da martani akan kisan mayakansa biyu da sojojin HKK su ka yi

A jiya talata ne dai sojojin haramtacciyar Kasar Isra'ila su ka kai hari akan wani sansanin dakarun Izzuddin al-qassam a garin Beit Lahiya,wanda ya yi sanadiyar shahadar biyu daga cikinsu. Kungiyar ta Hamas ta bayyana sunayen mutanen da cewa su ne; Ahmad Murjan, da Abduhafi al-Saylawi.

Kakakin kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas Fauzy Barhum ya dora alhakin kashe 'yan gwagwarmayar akan sojojin sahayoniya.

Barhum ya kara da cewa; Harin ta'addancin na 'yan sahayoniya ba zai raunana 'yan gwgawarmaya ba, za su fi gaba da fafutukar da suke yi. domin suna da karfin da za su mai da martani.