Saudiyya Ta Hana Shigar Da Makamashi Zuwa Ga Al'ummar Kasar Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33320-saudiyya_ta_hana_shigar_da_makamashi_zuwa_ga_al'ummar_kasar_yemen
A ci gaba da killace kasar Yemen da sojojin mamaya karkashin jagorancin Saudiyya suke yi, yanzu haka sun hana wani babban jirgin ruwa dauke da man fetur isa kasar ta Yemen.
(last modified 2018-09-24T14:08:08+00:00 )
Sep 24, 2018 14:08 UTC
  • Saudiyya Ta Hana Shigar Da Makamashi Zuwa Ga Al'ummar Kasar Yemen

A ci gaba da killace kasar Yemen da sojojin mamaya karkashin jagorancin Saudiyya suke yi, yanzu haka sun hana wani babban jirgin ruwa dauke da man fetur isa kasar ta Yemen.

Saudiyya ta hana wani jirgin ruwa dauke da man fetur da dangoginsa isa tashar jiragen ruwa ta gundumar Hudaidah a yammacin kasar Yemen.

Jirgin wanda yake dauke makamashi yana shirin tasowa ne daga gabar ruwa ta kasar Jibouti zuwa gabar ruwa ta Hudaidah, domin kai man fetur da dangoginsa da al'ummar kasar Yemen suke da matukar bukatuwa zuwa gare su.

Tun fiye da watanni biyu da suka gabata ne dai jiragen yakin Saudiyya suke ci gaba da yin lugudan wuta a kan birnin Hudaidai, inda a kwanakin baya kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bukacia  gudanar da bincike kan kisan wasu fararen hula iyalan gida da Saudiyya ta yi.