Ansarullah : An Kai Wa Filin Jirgin Saman Dubai Hari
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33416-ansarullah_an_kai_wa_filin_jirgin_saman_dubai_hari
Kungiyar Ansarullah ta Yemen wacce ake kira da 'yan Huthi ta tabbatar da kai wa filin saukar jiragen sama na Dubai hari a yau Lahadi.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 30, 2018 15:20 UTC
  • Ansarullah : An Kai Wa Filin Jirgin Saman Dubai Hari

Kungiyar Ansarullah ta Yemen wacce ake kira da 'yan Huthi ta tabbatar da kai wa filin saukar jiragen sama na Dubai hari a yau Lahadi.

Kakakin kungiyar, Muhammad Abdussalam ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Hadaddiyar Daular Larabawan ba za ta iya ci gaba da karyata kai wa filin saukar jiragen sama na Dubai hari ba.

Abdussalam ya ci gaba da cewa; Harin na yau shi ne na biyu a cikin wata guda da dakarun na Yemen su ka kai wa filin saukar jiragen sama na Dubai hari, kuma shakka babu ya haddasa tsaiko na tafiyar aiki.

A ranar 27 ga watan Agusta ne dai dakarun Ansarullah na Yemen su ka kai harin farko akan filin saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Dubai.