Rasha Ta Mikawa Siriya Makamin Kariya Samfarin S-300
Ministan tsaron kasar Rasha Sergey Shoygu ya sanar jiya Talata a taron majalisar tsaron kasar cewa kasarsa ta tamallakawa gwamnatin Bashar Al'Assad na Siriya makaman garkuwa na hare haren sama kirar S-300
A yayin taron tsaron kasar da ya gudana jiya Talata bisa jagorancin shugaban kasar Rasha, Viladimin Putin, mista Shoygu ya kara da cewa ko baya da wannan makami, kasar ta mallakawa kasar ta Siriya wasu sabin na'urori na musaman domin karfafa tsaron kasar.
Ministan tsaron kasar ta Rasha ya ce tuni suka fara koyar da sojojin Siriyan yadda za su yi amfani da wadannan makamai gami da sabin na'urorin, duk kuwa da cewa aikin koyarwar zai kwashe watani uku ana gudanar da shi.
A watan Satumbar da ya gabata ne kasar Rasha ta yanke shawarar mallakawa kasar Siriya makaman garkuwa na hare haren sama kirar S-300, bayan harbo wani jirgin yakinta a lardin Lazikiyya na kasar Siriya, lamarin da ya yi sanadiyar hallakar Sojojin Rashan 15.
Makaman kariyar kirar S-300 da wadannan sabin na'urorin soja dai zasu taimakawa Siriyan wajen kare kanta daga hare haren zaluncin da HK isra'ila ta jima tana kai mata.
Ko baya ga hakan Rasha ta ce zata dagula duk wasu hanyoyin sadarwa na jirgin Israila da ya kai hari Siriya, wanda masana ke ganin babban kalubale ne ga Israila.