Jiragen Kawancen Saudiya Sun Kahe Yamaniyawa 5
A wani Sabon Harin ta'addanci da jiragen kawancen saudiya suka kai lardin Jabana na jahar Hudaidai, kimanin yamaniyawa 5 ne suka yi shahada sannan wasu shida na daban suka jikkata.
Kamfanin dillancin labaran Saba'i na kasar Yemen ya habarta cewa jiragen yakin kawancen saudiya sun yi ruwan makamai masu linzami a lardin Jabana na jahar Hudaidaih,da kuma yankunan Bur'a da Mazra'a na lardin Marawi'a dake kan iyakan kasar da Saudiya, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar mutum 5 da kuma jikkatar wasu 6 na daban.
Har ila yau sojojin hayar Saudiya sun ruwan rokoki masu yawa a kauyukan dake kan iyakar Shida dake jahar Sa'ada na arewacin kasar ta Yemen, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar wani farar hula guda.
A wani hari kuma da jiragen yakin kawancen saudiyan suka kai kauyukan Razeh na jahar Sa'adah ya janyo hasara mai yawa ga dukiyoyin al'ummar yankin.
A matsayin mayar da martani, sojoji da dakarun sa kai na kasar ta yemen sun kai farmaki kan sansanin sojojin hayar saudiya na kudancin Attahiyata na jahar Hudaidah, tare da hallaka da kuma jikkata wani adadi daga cikinsu.
Tun a shekarar 2015 kasar Saudiyya da kawayenta musaman hadadiyar daular larabawa suka fara kai hari akan kasar Yemen tare da cikakken goyon bayan Amurka, inda suka killace kasar ta sama, ruwa da kuma ta kasar
kawo ya zuwa yanzu harin ya ci fiye da rayuka mutum 14,000 da kuma jikkata wasu dubai tare da raba wasu milyoyi da mahalinsu bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.