Majalisar Dattawan Amurka Tana Shirin Kakabawa Hizbullah Sabbin Takunkumai
Komitin bankuna na kasar Amurka a majakisar dattawan Amurka tana shirin kakabawa kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sabbin takunkumai.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha daga birnin Washington ya nakalto shugaban komitin bankuna na majalisar dattawan Amurak Mike Crop yana fadar haka a jiya jumma'a, ya kuma kara da cewa takunkuman zasu hada da kungiyar ta Hizbullah da kuma kasashen da suke goya mata baya , har'ila yau da wasu daddainkun mutane masu goyon bayanta a wajen kasar Lebanon.
Dukkan wakilan majalisar dattawan Amurka suna goyon bayan wannan shirin, amma hakan ba zai tabbata ba sai tare da amincewar shugaban kasa Donal Trump.
Kungiyar hizbullah dai, kungiyar ce wacce ta sami nasara korar HKI daga kasar Labanon bayan mamayarta na tsawon shekaru masu yawa, sannan tana daga cikin wadanda suka yaki yan ta'adda masu samun goyon bayan Amurka a Syria da kuma Iraqi.