Kungiyar 'Yan Jaridun Larabawa Ta Bukaci A Hukunta Makisan Kashoggi.
Kungiyar 'yan jaridu ta kasashen Larabawa ta bukaci a hukumta mutanan da suka kashe dan jaridan na kasar Saudiya Jamal Kashoggi.
A cikin wata sanarwa da kungiyar 'yan jarida ta kasashen Larabwa ta fitar a jiya Lahadi, ta bukaci a gudanar da bincike kan wadanda suka hallaka Jamal Khashoggi babban Dan jaridar nan mai sukan manufofin masarautar saudiya, sannan kuma a gurfanar da su a gaban kotu.
Sanarwar ta yi ishara kan masu kokarin boye gaskiya kan abinda ya wakana ga Dan jaridar, tare da neman su su gaggauwa bayyana gaskiyar abinda ya wakana a game dan jaridar na kasar Saudiya Jamal Khashoggi.
Sakamakon farko na binciken da 'yan sandan kasar Turkiya suka gudanar kan bacewar fitaccen dan jaridar Saudiyya mai sukar gwamnati na nuni da cewa, an kashe shi ne a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul.
mahukuntan kasar Turkiya sun bayar da tabbacin cewa Jamal Khashoggi bai fita daga karamin ofishin jakadancin Saudiyya ba, tun bayan da ya shiga cikin ofishin a ranar 2 ga watan oktoban da ta gabata.