Yemen: Mutane Miliyan 12 Na Fuskantar Rashin Abinci
Shugaban hukumar abinci ta duniya ( WFP) ya fada a jiya Litinin cewa; Da akwai mutane miliyan 12 a kasar Yemen da suke fuskantar karancin abinci
Stephen Adnerson wanda tashar talabijin din CNN ta yi hira da shi, ya bayyana cewa; Wani adadin na mutane da ya kai mutane miliyan 18 ba su da wuraren da za su rika samun abinci
Anderson ya kuma kara da cewa; matukar yakin kasar ta Yemen ya ci gaba, to shakka babu al'ummar kasar baki daya za ta fuskanci yunwa matsananciya.
Kasar Yemen tana fama da yaki wanda kasar Saudiyya take jagoranta, tun daga 2015. Kawo ya zuwa yanzu mutane 14,000 ne su ka kwanta dama sanadiyyar yakin, yayin da wasu dubun bubata su ka jikkata.
Bugu da kari, yakin na haddasa asara ta dukiya da kuma barnata muhimman cibiyoyi na gwamnati da su ka hada da asibitoci da wuraren shan magani.