Dakarun Yemen Sun Hallaka Sojojin Hayar Saudiya Da Dama
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33655-dakarun_yemen_sun_hallaka_sojojin_hayar_saudiya_da_dama
Dakarun tsaron yemen sun kai wani hari kan sojojin hayar Saudiya da jirgi maras matuki a Duraihimi dake gabar ruwan yammacin kasar tare da hallaka da dama daga cikinsu.
(last modified 2018-10-16T15:40:54+00:00 )
Oct 16, 2018 15:40 UTC
  • Dakarun Yemen Sun Hallaka Sojojin Hayar Saudiya Da Dama

Dakarun tsaron yemen sun kai wani hari kan sojojin hayar Saudiya da jirgi maras matuki a Duraihimi dake gabar ruwan yammacin kasar tare da hallaka da dama daga cikinsu.

Tashar Talabijin din Almasira ta kasar Yemen ta habarta cewa a wani harin hadin gwiwa da injiniyoyi na sojojin Yemen tare da dakarun sa kai na kasar sun kai kan wata mota dauke da  sojojin hayar saudiya,a yammacin Tahtiyah dake yankin Duraihim  sun samun nasarar hallaka dukkanin sojojin dake cikin motar.

A bangare guda kuma Dakarun na yemen sun dakile wani farmaki na mamayar Sojojin hayar saudiya a yammacin yankin His dake gabar ruwar yammacin kasar.

Kamar yadda kuma Dakarun sa kai na kasar ta Yemen suka kai wani mumunan farmaki kan Sojojin hayar ta saudiya a wani sansaninsu dake da nisan kilomita 16 daga gabar ruwan yammacin inda suka hallaka da dama daga cikinsu.

Tun a watan Maris na 2015 ne kasar Saudiya bisa goyon bayan Amurka da hadaddiyar daular Larabawa suka fara kai harin wuce gona da iri kan Al'ummar kasar Yemen, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 14 da kuma jikatta wasu dubai na daban tare da raba wasu milyoyi da gidajensu.