Wani Bafalastine Ya Yi Shahada A Yau A Yankin Zirin Gaza
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33663-wani_bafalastine_ya_yi_shahada_a_yau_a_yankin_zirin_gaza
A ci gaba da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri da Isra'ila ke yi kan al'ummar Palastine,a yau wani bafalastine guda ya yi shahada a Gaza.
(last modified 2018-10-17T08:48:02+00:00 )
Oct 17, 2018 08:48 UTC
  • Wani Bafalastine Ya Yi Shahada A Yau A Yankin Zirin Gaza

A ci gaba da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri da Isra'ila ke yi kan al'ummar Palastine,a yau wani bafalastine guda ya yi shahada a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa, Isra'ila ta kai harin ne da jirgi marassa matuki a cikin Gaza, inda ta kashe wani bafalastine mai suna Muhammad Za'anin mai shekaru 25 a cikin zirin gaza.

Wannan mataki na Isra'ila na ziwa ne a daidai lokacin da take ta kara tsananta hare-harenta kan al'ummar Palastine yankunan zirin Gaza da kuma gabar yama da kogin Jordan.

Koa  ranar Juma'a da ta gabata Isra'ila ta kashe Falastinawa 7 a yankin Zirin Gaza a gangamin da ake gunarwa na neman hakkokin Falastinawa da aka kora daga yankuannsu aka tilasta musu yin gudun hijira, domin su samu dawuwa kaarsu ta haihuwa.