Iraki : An Kammala Daukar Dukkanin Matakan Tsaro Domin Tarukan Arbaeen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33671-iraki_an_kammala_daukar_dukkanin_matakan_tsaro_domin_tarukan_arbaeen
Mahukuntan kasar Iraki sun sanar da cewa an kammala daukar dukkanin matakan da suka kamata ta fuskar tsaro domin tarukan Arbaeen da za a gudanar a kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Oct 18, 2018 02:21 UTC
  • Iraki : An Kammala Daukar Dukkanin Matakan Tsaro Domin Tarukan Arbaeen

Mahukuntan kasar Iraki sun sanar da cewa an kammala daukar dukkanin matakan da suka kamata ta fuskar tsaro domin tarukan Arbaeen da za a gudanar a kasar.

Kamfanin dillancinSaumaria News ya bayar da rahoton cewa, manyan jami'an tsaron cikin gida na kasar Iraki sun gudanar da zama, domin tattauna yanayin matakan tsaro a  tarukan Arbaeen da za a gudanar a kasar.

Rahoton ya ce taron wanda ya gudana a karkashin ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Iraki, ya gamsu da irin matakan da aka dauka ya zuwa yanzu, domin makonni kafin lokacin fara tarukan na Arbaeen, dubban jami'an tsaro suka fara gudanar da ayyukansu a ciki da wajen birnin Karbala.

Taron Arbaeen na cikar kwanaki 40 da shahadar Imam Hussain (AS) a halin yanzu dai shi ne taro mafi girma da ake gudanarwa a duniya, wanda ya kan hada mutane fiye da miliyan 20 a lokaci guda a birnin Karbala.