Turkiyya: An Sake Binciken Karamin Ofishin Jakadancin Saudiyya A Santanbul
Masu gudanar da bincike kan bacewar dan jaridar kasar Saudiyya Jamal Khashoggi, bayan shigarsa cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul sun sake komawa ofishin domin ci gaba da bincike.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, bayan bincike na tsawon sa'oi 9 da jami'an Turkiya suka gudanar a ranar Litinin da ta gabata a karamin ofishin jadakancin Saudiyya a Istanbul, a jiya ma sun sake komawa inda suka bincika motocin da suke wurin da na'urorin daukar kaya.
Jaridar Yeni Safak ta kasar Turkiya da take da kusanci da gwamnatin kasar ta bayar da rahoton cewa, ta samu bayanai da ke tabbatar da cewa, masu binciken sun samu dalilai da suke tabbatar da cewa an kashe Jamal Khashoggi ne a cikin karamin ofishin jakadancin na Saudiyya da ke Istanbul.
Da farko dai Saudiyya taki amincewa da a gudanar da bincike kan batun bacewar Khashoggi a cikin ofishin nata, amma daga bisani bayan shudewar makonni biyu sakamakon matsin lambar da take fuskanta daga kasashen duniya kan batun, ta amince da a yi binciken, tana mai nisanta kanta da duk wani abu da ya faru da Khashoggi.