Saudiyya Ta Amsa Kashe Dan Jarida Jamal Kashoggi
Sanarwa ta kuma kara da cewa; Fada ne ya barke a tsakanin Jamal Kashoogi da mutane 15 'yan Saudiyya da suke yi masa tambayoyi, abin da a karshe ya kai ga mutuwarsa.
Kamfanin dillancin labarun Saudiyya wanda ya dauki labarin ya kuma sanar da cewa an kame wasu mutane 18 domin yin bincike. Bugu da kari an dakatar da wasu jami'an tsaron daga ayyukansu daga cikinsu hadda Ahmad Asiry, mataimakin shugaban hukumar leken asirin kasar.
Har ila yau, dakatarwa daga aikin ta shafi Sa'ud al-Qahdhani wanda daya ne daga cikin manyan masu bada shawara a fadar gidan sarautar kasar.
A can Amurka, babbar kawar Saudiyya, shugaba Donald trump ya bayyana alamar gasmsuwa da riwayar ta Saudiyya akan abin da ya faru, sai dai ya ce zai yi aiki tare da Majalisar dokokin kasar domin daukar matakin da ya dace akan Saudiyya.