Jiragen Yakin Sahayuna Sun Yi Lugudan Wuta A Yankin Zirin Gaza.
A daren jiya juma'a jiragen yakin Sahayuna sun kai hari da makamai masu Linzami a yankin zirin Gaza.
Majiyoyin Palastinu sun habarta cewa a daren jiya juma'a jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hari wuraren kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa a yankin Baitu-Lahiya dake arewaci da kuma yankin Khan Yunus na kudancin yankin na zirin Gaza.
Har ila yau wani jirgin yaki masar matuki na Sahayunan ya kai hari kan wani filin Noma dake kusa da mashigar Karam Abu Salim dake kudu maso gabashin zirin Gaza.
Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana irin hasarar da wannan hari ya janyo.
A daren larabar da ta gabata, Sojojin Sahayuna sun buda wuta kan wasu gungun Palastinawa a gabashin Rafah na kudancin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar jakkatar mutum takwas.