Arba'in : Firaministan Iraki Ya Jinjinawa Dakarun Hashadu-Sha'abi
Piraministan kasar Iraki ya jinjinawa dakarun sa kai na Hashadu-Sha'abi a game da yadda suka tabbatar da tsaro da kuma kare rayukan milyoyin maziyartan Imam Husain(a.s) a taron Arba'in.
A yayin ziyarar da kai birnin Karbala'a a wannan Litinin, Piraministan kasar Iraki Adil Abdul-Mahadi ya gana da dukkanin komondojin tsaron kasar da kuma na sa kai Hashadu-Sha'abi dake aikin tabbatar da tsaro tare da kare rayukan masu ziyarar Hubbarin Imam Husain jikan Ma'aikin Allah (s.a.w.a), inda suka yi masa bayyani dalla-dalla kan irin ayyukan da suke gudanarwa domin tabbatar da tsaro, Piraministan ya jinjinawa dukkanin jami'an tsaron dake gudanar da ayyukansu a wannan wuri mai tsarki.
Iyakokin kasar ta Iraki na karbar milyoyin muminai ko wata shekara a irin wadannan ranaiku na zagayowar arab'in Iman Husain (a.s) jikan ma'aikin Allah (s.a.w.a).
Maziyartar kasar Iraki daga sassa daban-daban na cikin kasar na tattaki ba tare da sun sanya takalma a kafafuwansu ba har zuwa hubbarin Imam Husain (a.s) domin girmamawa.
Ranar 30 ga watan Oktaba na wannan shekara ta 2018, rana ce da ta yi daidai da ranar 20 ga watan Safar na shekara 1440 hijra kamariya, ranar jagayowar arba'in din shahadar Imam Husain (a.s) Imami na uku daga cikin limaman shiriya 12 na iyalan gidansa tsarkaka da kuma sahabansa a filin karbala.