Kungiyar 'Yanto Palasdinu Ta Bukaci ICC Ta Binciki Kisan Palasdinawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33839-kungiyar_'yanto_palasdinu_ta_bukaci_icc_ta_binciki_kisan_palasdinawa
Kungiyar 'Yanto Palasdinu ta PLO ta bukaci kotun da ke shari'ar manyan laifuka a duniya ta ICC da ta gudanar da bincike kan mutuwar wasu matasan Palasdinawa uku a yankin Zirin Gaza.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Oct 30, 2018 02:45 UTC
  • Kungiyar 'Yanto Palasdinu Ta Bukaci ICC Ta Binciki Kisan Palasdinawa

Kungiyar 'Yanto Palasdinu ta PLO ta bukaci kotun da ke shari'ar manyan laifuka a duniya ta ICC da ta gudanar da bincike kan mutuwar wasu matasan Palasdinawa uku a yankin Zirin Gaza.

A bayanin da kungiyar 'yanto Palasdinu ta PLO ta fitar a jiya Litinin yana dauke da cewa: Kungiyar PLO tana kira ga kungiyoyin kasa da kasa musamman kotun da ke shari'ar manyan laifuka ta duniya ta International Criminal Court da ke birnin Hague na kasar Netherland ya dauki matakin gudanar da bincike kan mutuwar wasu matasan Palasdinawa uku sakamakon harin wuce gona da irin da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai musu a garin Deir al-Balah da ke yankin Zirin Gaza na Palasdinu.

A yammacin ranar Lahadi ne jirgin saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya yi luguden wuta kan wasu matasa Palasdinawa uku a yankin gabashin garin Deir al-Balah da ke yankin Zirin Gaza, kuma sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka hana kai musu dauki ceto rayuwarsu lamarin da ya janyo shahadarsu.

Tun a ranar 1 ga watan Aprilun shekara ta 2015 ne Palasdinu ta kasance mamba a jerin kasashen da suka amince da kotun da ke shari'ar manyan laifuka a duniya ta ICC, kuma tana ci gaba da kokarin ganin kotun ta dauki matakin bin kadin Palasdinawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila take zalunta tsawon shekaru.