Yemen: Zanga-zangar Nuna Kin Amincewa Da Mamayar Saudiyya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33902-yemen_zanga_zangar_nuna_kin_amincewa_da_mamayar_saudiyya
Mazauna garin al-Muhrah da ke gabacin kasar Yemen sun yi Zanga-zangar yin kira ga sojojin Saudiyya da su fice daga kasar
(last modified 2018-11-03T08:55:00+00:00 )
Nov 03, 2018 08:55 UTC
  • Yemen: Zanga-zangar Nuna Kin Amincewa Da Mamayar Saudiyya

Mazauna garin al-Muhrah da ke gabacin kasar Yemen sun yi Zanga-zangar yin kira ga sojojin Saudiyya da su fice daga kasar

Da marecen jiya juma'a ne mazauna garin na Muhrah su ka gudanar da Zanga-zangar suna masu yin tir da duk wani yunkuri na raunana hurumi da 'yancin kasar Yemen da cin gashin kanta

A gefe daya jiragen yakin Saudiyya da na Hadaddiyar Daular Larabawa suna ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na kasar da su ka hada da al-Hudaidah.

A shekarar da ta gabata ne dai sojojin na Saudiyya da na Hadaddiyar Daular Larabawa su ka bude sansani a yankin na al-Muhrah da sunan fada da fasa kwauri.

Yakin da Saudiyya ta shelanta a cikin kasar Yemen a 2015 ya shiga cikin shekara ta 4 ba tare da ta cimma wata manufa ba.