Nov 06, 2018 17:34 UTC
  • Hamas Ta Sha Alwashin Ci gaba Da Nuna Kin Jinin Isra'ila

Kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas ta ce za ta ci gaba da nuna kin jinin Haramtaciyar kasar Isra'ila har sai ta cimma gurinta.

Da yake sanar da hakan daya daga cikin jiga jigan kungiyar mai suna, Issam Daalees ya ce za su ci gaba da yin zanga zangar nuna kin amincewa da manufofin Isra'ila har sai sun cimma burinsu.

A daya bangare kuma da yake tsokaci game da yunkurin shiga tsakani wanda hukumar tattara bayanan sirri ta kasar Masar ke yunkurin shiryawa, Daalees ya ce za'a ci gaba da yin wancan yunkurin shi ma "har sai mun kai ga cimma matsaya wadda ta yi daidai da muradun al'ummarmu."

Wata tawagar kasar Masar ce ke shiga tsakani bangarorin biyu domin maido da tattaunawar sulhu tsakanin Palastinawa dangane da batun yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila.

Bayanai sun ce wakilan kasar Masar sun gudanar da tattaunawa tare da wasu manyan jami'an kungiyar Hamas da sauran shugabannin daya bangaren domin cimma matsaya na duba yiwuwar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar ta Hamas a zirin Gaza

Tags