Saudiyya Na Ci Gaba Da Kai Hari A Garin Hudaidah
Harin da Jiragen Yakin Saudiyyar su ka kai a yankin 7 ga watan Yuni, karamin yaro daya ya rasa ransa, yayin da wasu mutane 7 suka jikkata
Tashar talabijin din al-masirah ta ba da labarin cewa; A sanadiyyar harin na Saudiyya gidajen fararen hula da dama sun rushe tare da haddasa asara ga dukiyoyinsu.
A jiya alhamis ma dai sojojin na Saudiyya sun kai wasu hare-haren har sau 30 a yankin da kae kira Kilo 60 da kuma babban titin Sittin da suke a cikin birnin na Hudaidah.
Garin al-Hudaidah yana da matukar muhimmanci saboda tashar jirgin ruwan da take cikinsa wacce ake shigar da kayan abinci cikin kasar da kaso 70%
Harin da Saudiyyar take kai wa a birnin Hudaidah yana samun cikakken goyon bayan sojojin Amurka da na Birtaniya kamar yadda kafafen watsa labarun Amurka suka ambata.
A cikin shekaru uku na yakin da Saudiyya ta shelanta akan Yemen fiye da mutane 13,000 su ka kwanta dama, yayin da wasu dubbai su ka jikkata.
Bugu da kari, hare-haren na Saudiyya sun yi sanadiyyar lalata asibitoci da cibiyoyin shan magani kamar kuma yadda su ka jefa kasar cikin yunwa saboda rashin abinci.