Sojojin Yemen Sun Halba Makamai Mai Linzami Zuwa Lardin Marib
Sojoji da dakarun sa kai na kasar Yemen sun harba makamai mai linzami zuwa sansanin sojojin hayar saudiya dake yammacin jahar Marib na tsakiyar kasar
A safiyar wannan asabar, sojoji da dakarun sa kai na kasar yemen sun sanar da halba makami mai linzami safanin zilzal na daya zuwa sanasanin sojojin hayar saudiya a jahar marib, tare da tabbatar da cewa makamin ya sauka a daidai inda aka bukata, kuma wannan hari ya yi sanadiyar hallaka da kuma jikkata sojojin hayar na saudiya da dama.
Major Janar Ali Mushaki mataimakin babban komandan sojojin kasar ta Yemen ya ce sojojin kasar sun dauki alkawarin cewa ba za su bar ko wani sojin mamaya fitar daga cikin kasar a raye ba.
Duk da irin killacewar da aka sojojin hayar saudiya suka yi wa kasar ta Yemen, amma ko wata rana sojoji da dakarun sa kai na kasar na kara samun nasara wajen kara karfin makaman kariyarsu.
Tun a 2015 ne dai sojojin na kasar Saudiyya suka fara kai hari akan kasar Yemen tare da cikakken goyon bayan Amurka, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci fiye da rayuka 12,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.