Isra'ila : Gwamnatin Netanyahu Ta Shiga Cikin Rudani
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34098-isra'ila_gwamnatin_netanyahu_ta_shiga_cikin_rudani
Gwamnatin Fira ministan H.K Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ta fada cikin wani rudani bayan da ministan tsaron yahudawan ya sanar da yin murabus daga mukaminsa.
(last modified 2018-11-15T02:23:02+00:00 )
Nov 15, 2018 02:23 UTC
  • Isra'ila : Gwamnatin Netanyahu Ta Shiga Cikin Rudani

Gwamnatin Fira ministan H.K Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ta fada cikin wani rudani bayan da ministan tsaron yahudawan ya sanar da yin murabus daga mukaminsa.

A jiya Laraba ne ministan tsaron yahudawan mamaya na Isra'ilar Avigdor Lieberman, ya sanar da yin murabus, bayan da gwamnatin Netanyahu ta amince da tsagaita wuta da kungiyar Hamas, bayan rikicin baya baya nan wanda Hamas tayi wa Isra'ilar ruwan rokoki sama da 300. 

Koda yake wasu daga cikin kusoshin jam'iyyar Likoud ta Netanyahu sun ce, har yanzu Lieberman bai gabatar da takardar murabus dinsa ba, amma tuni fira ministan ya fara nazari kan batun, tare da kore jita jitan cewa netanyahun ya fara tunanin kafa kawancen game da shirin kiran zaben kafin wa'adi. 

Kafin hakan dama wasu majiyoyi a jam'iyyar ta Likoud sun bayyana cewa akwai yiyuwar Netanyahu ya dauki mukamin ministan tsaron baya ga na kula da harkokin waje da ya ke dauke da.

Kungiyar Hamas dai ta danganta murabus din ministan tsaron Isra'ilar da babbar nasara a gare ta, a yayin da shi kuwa ya danganta cimma yarjejeniyar tsagaita da Hamas din da gwamnatin Netanyahu ta yi da durkusawa gaban 'yan ta'adda.