Dakarun Tsaron Yemen Sun Kai Hari Kan Sansanin Sojojin Hayan Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34118-dakarun_tsaron_yemen_sun_kai_hari_kan_sansanin_sojojin_hayan_saudiya
Dakarun tsaron saman kasar Yemen sun kai hari kan sansanin sojojin hayar saudiya da jirgin yaki maras matuki a jahar Marib dake tsakiyar kasar
(last modified 2018-11-16T15:36:38+00:00 )
Nov 16, 2018 15:36 UTC
  • Dakarun Tsaron Yemen Sun Kai Hari Kan Sansanin Sojojin Hayan Saudiya

Dakarun tsaron saman kasar Yemen sun kai hari kan sansanin sojojin hayar saudiya da jirgin yaki maras matuki a jahar Marib dake tsakiyar kasar

Kamfanin dillancin labaran yemen (Saba) ya habarta cewa a wannan dakarun tsaron sararin samaniyar kasar sun kai hari da jirgin yaki maras matuki samfarin Qasef 1 zuwa sansanin sojojin hayar saudiya dake jahar Marib lamarin da ya janyo hasarar rayuka gami da dukiya ga 'yan koran saudiyar.

A bangare guda kakakin gwamnatin ceto kasar ta yemen Daifullahi Ash-shami ya ce da'awar da kawancen saudiya ke yi na cewa an cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta a kasar ta Yemen ba gaskiya ba ne, sun yi wannan da'awa ne domin kawar da hankulan Al'ummar Duniya sakamakon matsin lambar da suke fuskanta daga kungiyoyin kasa da kasa.

Ash-shami ya kara da cewa har yanzu jiragen kawancen saudiya na ci gaba da kisan kare dangi kan al'ummar kasar ta yemen tare da rusa duk wani gine-ginen kasar musaman ma a gabar ruwan yammacin kasar.

Tun a 2015 ne dai sojojin na kasar Saudiyya suka fara kai hari akan kasar Yemen tare da cikakken goyon bayan Amurka, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci fiye da rayuka 14,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.