Kananan Yara Masu Yawa Ne HKK Ta Kashe A Shekarar Bana
Wata cibiyar kare hakkokin kananan yara ta Palasdinawa ta ce a cikin wannan shekara ta 2018 kadai, adadin yaran palasdinawan da su ka yi shahada suna da yawa
Kamfanin dillancin labarun Anatoli ya ambato wani rahoto da kungiyar kare hakkokin kananan yara palasdinawa ta fitar a jiya Litinin, in dda ta ce; Adadin kananan yaran da su ka yi shadarar a shekarar bana sun kai 52
Rahoton ya ci gaba da cewa; Sojojin hamratacciyar kasar Isra'ila sun kashe yaran ne a yankunan Gaza da yammacin kogin Jordan.
Rahoton da aka fitar adaidai lokacin da ake tunawa da ranar kare hakkokin kananan yara ta duniya ya kuma kara da cewa 48 daga cikin yaran da aka kashe sun fito ne daga yankin zirin Gaza, yayin da sauran 6 su ka fito daga yammacin kogin Joedan.
A halin da ake ciki a yanzu da akwai kananan yara da adadinsu ya kai 350 wadanda ake tsare da su a gidajen kurkukun haramtacciyar Kasar Isra'ila.