Afghanistan: Ana Zaman Makokin Na Juyayin Harin Mauludi
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34175-afghanistan_ana_zaman_makokin_na_juyayin_harin_mauludi
Gwamnatin kasar Afghanistan ta sanar da zaman makoki na gama gari saboda juyayin mutanen da su ka rasa rayukansu sandiyyar harin da aka kai musu a yayin bikin Mauludin manzon Allah (s.a.w.a)
(last modified 2018-11-21T04:43:22+00:00 )
Nov 21, 2018 04:43 UTC
  • Afghanistan: Ana Zaman Makokin Na Juyayin Harin Mauludi

Gwamnatin kasar Afghanistan ta sanar da zaman makoki na gama gari saboda juyayin mutanen da su ka rasa rayukansu sandiyyar harin da aka kai musu a yayin bikin Mauludin manzon Allah (s.a.w.a)

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Afghanistan ta sanar da cewa adadin mutane da suka kwanta dama sanadiyyar hairn da aka kai musu ya kai 50, yayin da wasu da adadinsu ya kai 72 su ka jikkata.

Majiyar ta kuma tabbatar da cewa mutane 24 daga cikin suna suka jikkata suna cikin matsanancin hali, lamarin da zai iya kara yawan wadanda suka rasa rayukansu.

Ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran da yake a birnin Kabul ya yi tir da harin na ta'addanci wanda ya dauki rayukan malaman addinin musulunci da dama da suke halartar taron na Mauludi.

Bugu da kari ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran din ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnati da kuma al'ummar Afghanistan.