Afganistan : Amurka Ta Hallaka Babban Kwamandan Taliban
Rahotanni daga Afganistan na cewa wani jirgin Amurka marar direba, ya hallaka wani babban kwamandan mayakan kungiyar taliban, mai suna Abdul Rahim Manan, a lardin Helmand dake kusa da iyaka da Kandahar.
Majiyoyi daga kungiyar tsaro ta NATO da hukumomin kasar ta Afgasnitan duk sun tabbatar da kisan na wannan kwamandan kungiyar ta taliban tare da wasu mayaka 32.
Ita mai da kungiyar ta Taliban ta tabbatar da hakan wanda ta danganta da babbar hasara gare ta.
Kakakin gwamnan lardin na Helmand, Omar Zwak, ya bayyana cewa kwamandan na kungiyar ta Taliban ya mutu a asibiti sakamakon munanen raunukan da ya samu a harin da aka kai ma tawagarsa da yammacin jiya Asabar.
Abdul Rahim Manan dai na daga cikin jerin sunayen wadanda ke taimaka wa 'yan ta'adda da kasashen da suka hada da Amurka, Saudiyya, da wasu kasashen yankin Golfe biyar suka fitar a ranar 23 ga watan Oktoba da ya gabata, tare toshe kaddarorinsu.