Kungiyoyin Palasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Rushe Gidajen 'Yan Gwagwarmaya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34474-kungiyoyin_palasdinawa_sun_yi_allah_wadai_da_rushe_gidajen_'yan_gwagwarmaya
Mai magana da yawun kungiyar gwagwarmayar musulunci Hamas rushe gidajen 'yan gwgawarmaya da kuma yi musu barazanar kora, yana nuni da yadda haramtacciyar kasar Isra'ila ta ci kasa ne a agban al'ummar palasdinu
(last modified 2018-12-18T03:59:54+00:00 )
Dec 18, 2018 03:59 UTC
  • Kungiyoyin Palasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Rushe Gidajen 'Yan Gwagwarmaya

Mai magana da yawun kungiyar gwagwarmayar musulunci Hamas rushe gidajen 'yan gwgawarmaya da kuma yi musu barazanar kora, yana nuni da yadda haramtacciyar kasar Isra'ila ta ci kasa ne a agban al'ummar palasdinu

Abdullatif al-qanui ya kara da cewa; Rushe gidajen da 'yan Sahayoniya suke yi ba zai hana samarin yankin yammacin kogin Jordan yi gwagwarmaya ba, kamar yadda barazanar da 'yan sahayoniyar suke yi wa iyalan 'yan gwagwarmaya ba za ta raunana su ba.

Ita ma kungiyar Jihadul Islami ta yi tir da rushe gidajen 'yan gwgawarmaya da haramtacciyar kasar Isra'ilan take yi tare da cewa babu inda zai kai haramtacciyar kasar Isra'ila

Pira ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamine Natenyahu ya ba da umarnin rushe gidajen iyalan Palasdinawan da su ka kai hare-haren daukar fansa akan 'yan Sahayoniya