Tarayyar Turai Ta Damu Da Yadda HKK Ke Rusa Makarantun Palasdinawa
A wani bayani da tarayyar turai din ta fitar ta hanyar ofishinta da yake a Hkk ta bayyana damuwa akan yadda 'yan sahayoniyar suke ci gaba da rusa makarantun palasdinawa
Ofishin Tarayyar turai a Palasdinu da take a karkashin mamaya ya yi ishara da makarantar "al-Tahaddi 13" da 'yan sahayoniya su ka rusa a garin al-khalil a ranar 5 ga wannan watan na Disamba, sannan ya bayyana cewa; Wannan shi ne karo na biyar a cikin 2018 da 'yan sahayoniyar su ka rusa makarantun Palasdinawa
Har ila yau bayanin ya ce ya zuwa yanzu an rusa da kuma rufe makarantun da adadinsu ya kai 50 a cikin yammacin kogin jordan da Kudus, da hakan ya shafi yan makaranta 50,000.
Ofishin n aTarayyar turai ya yi kira da a dakatar da rushe ko rufe makarantun Palasdinawa haka nan gina matsugunan yahudawa 'yan share wuri zauna.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Tarayyar turai din ta yi kira ga haramtacciyar kasar Isra'ila da ta dakatar da gina matsugunan Yahudawa 'yan share wuri zauna ba, sai dai har yanzu babu alamar 'yan sahayoniyar za su daina