Trump: Gwamnatin Saudia Zata Biya Kudaden Sake Gina Kasar Siriya
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa gwamnatin kasar Saudia ta dauki alkawarin zata bada kudade don sake gina kasar Siriya a madadin gwamnatinsa.
Kamfanin dillancin labaran Farenews na kasar Iran ya nakalto shugaba Trump yana fadar haka a shafinsa na tweeter a jiya litinin, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Saudia zata bada kudaden sake gida kasar Siriya bayan an kawo karshen kungiyar yan ta'adda ta Daesh a kasar.
Wannan bayanan da shugaba Trump suna zuwa ne kwanaki kadan bayan da ya bada sanarwan cewa gwamnatinsa zata janye sojojinta daga kasar Siriya.
Tun shekara ta 2011 ne kungiyoyin yan ta'adda, da dama wadanda suka hada har da kungiyar Daesh suka mamaye yankuna masu yawa a kasar Siriya da nufin kifar da gwamnatin shugaban Bashar al-asad amma bayan shekaru kimani 7 sun kada yin haka duk tare da tallafin da suke samu daga kasashen yamma musamman ita kasar Amurka.