An Cafke Masu Zanga-zanga 10,500 A Bangladesh
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34569-an_cafke_masu_zanga_zanga_10_500_a_bangladesh
Jam'iyyun adawa a Bangaladesh sun ce 'yan sanda a kasar sun cafke masu da magoya baya sama da 10,500 a makwannin baya bayan nan.
(last modified 2018-12-25T13:35:00+00:00 )
Dec 25, 2018 13:35 UTC
  • An Cafke Masu Zanga-zanga 10,500 A Bangladesh

Jam'iyyun adawa a Bangaladesh sun ce 'yan sanda a kasar sun cafke masu da magoya baya sama da 10,500 a makwannin baya bayan nan.

Jam'iiyun adawan sun danganta lamarin da wani yunkuri na haddasa fargaba a zukatan jama'a gabanin zaben kasar dake tafe.

Babbar jam'iyya adawa ta kasar BNP wacce jagorarta, Khaleda Zia ke zama gidan yari ta ce an cafke masu da magoya baya 7,021.

Ita kuwa jami'yyar islama ta Jamaat-e-Islami, wacce aka haramta ma da tsayawa takara a zaben wacce kuma take kawance da babbar jam'iyyar adawa ta BNP, cewa tayi ana tsare mata da magoya baya sama da 3,500.

Jami'an tsaro 30,000 ne aka jibge a ranar Litini domin tabbatar da doka da oda, a wannan kasa dake da mafi yawan al'umma Miliyan 165 mafi yawa musulmi, saidai a cewar jam'iyyar ta BNP hakan bai shawo kan matsalar ba, hasali ma ko wacce rana ana cafke masu maogaya baya 80 zuwa 90. 

Saidai wani kakakin 'yan sanda a kasar ya ce basu cafke mutane haka kawai, kuma duk wanda aka cafke an cafke shi tare da sammaci, amma bai tabbatar da adadin mutanen da aka ambata cewa an cafke ba. 

Amurka dai ta bukaci gwamnatin fira ministar kasar, Sheikh Hasina,dake neman wa'adi na hudu data tabbatar da yin haske a zaben na ranar Lahadi mai zuwa.