Amurka Ta Kafa Wasu Sabbin Sansanonin Soja A Kasar Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34571-amurka_ta_kafa_wasu_sabbin_sansanonin_soja_a_kasar_iraki
Wani dan majalisar yankin Anbar na kasar Iraki ne ya bayyana cewa; Amurkan ta kafa sabbin sansanonin soja biyu a kusa da iyaka da kasar Syria
(last modified 2018-12-26T07:05:24+00:00 )
Dec 26, 2018 07:05 UTC
  • Amurka Ta Kafa Wasu Sabbin Sansanonin Soja A Kasar Iraki

Wani dan majalisar yankin Anbar na kasar Iraki ne ya bayyana cewa; Amurkan ta kafa sabbin sansanonin soja biyu a kusa da iyaka da kasar Syria

Kafa sabbin sansanonin ya zo ne kwanaki kadan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa; Amurka za ta janye dukkanin sojojinta daga kasar Syria mai makwabtaka da Iraki

Farhan Duilami wanda dan majalisa ne a yankin Anbar ya fadawa kamfanin dillancin labarun Anatoli cewa; Amurkan ta kafa sansani guda a yankin al-Rumana da ke garin al-qaim, a kusa da iyaka da kasar Syria, sai kuma wani sansanin a garin Ar-Rutbah, da ke yammacin garin Ramadi.

Farhan Dulaimi ya kara da cewa; Da akwai sojojin Amurka da jirage marasa matuki da Amukran ta girke a cikin sabbin sansanonin.