Taron Kasashen Iran, Turkiya Da Rasha Akan Kasar Syria
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34590-taron_kasashen_iran_turkiya_da_rasha_akan_kasar_syria
Za a yi taron ne dai a farkon sabuwar shekarar 2019 mai kamawa domin tattauna halin da kasar Syria ke ciki
(last modified 2018-12-28T08:31:03+00:00 )
Dec 28, 2018 08:31 UTC
  • Taron Kasashen Iran, Turkiya Da Rasha Akan Kasar Syria

Za a yi taron ne dai a farkon sabuwar shekarar 2019 mai kamawa domin tattauna halin da kasar Syria ke ciki

Kamfanin dillancin labarun France 24 ya ba da labarin cewa; A daidai lokacin da Amurka take shirin ficewa daga Syria, kasashen Iran, Turkiya da Rasha za su gudanar da taro a farkon makon sabuwar shekara, a birnin Moscow

 Mataimakon ministan harkokin wajen kasar Rasha Mikha'el Bagdanov ya ce; A wannan karon mu ne za su dauki nauyin taron.

Taro na karshe da shugabannin kasashen uku su ka yi, ya kasance a birnin Tehran a watan Satumba.