Yemen : 'Yan Houtsis Sun Fara Yanjewa Daga Tashar Ruwan Hodeida
Rahotanni daga Yemen na cewa 'yan gwagwarmaya na Houtsis sun fara janyewa daga tashar ruwan Hodeida, dake yammacin kasar, a wani mataki na ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a farkon watan Disanban nan a shiga tsakanin MDD.
Wani jami'in MDD, da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, 'yan Houtsis din fara janyewa daga yankin tun cikin daren jiya.
Shi ma da yake tabbatar da hakan wani jigo daga bangaren 'yan Houstis ya tababatar da hakan ga kamfanin dillancin labaren Saba.
Yarjejeniyar da aka cimma a Sweden a shiga majalisar dinkin duniya ta dai tanadi tsagaita wuta tsakanin bangarorin dake rikici a Yemen, domin bada damar shigar da kayan agaji dana abinci a yankin Hodaida.
Tun a cikin shekara 2014 ne 'yan Houtsis ke rike da yankin na Hodeida wanda dakarun dake biyaya ga gwamnatin kasar suka kaddamar wa farmaki da nufin sake kwato shi.
Yakin da kasar ta Yemen ta fada ya dai yi sanadin mutuwar mutane akalla 10,000 tun daga 2015, tare da jefa kasar cikin bala'i fami muni a duniya inji MDD.