Limamin Tehran: Gabas Ta Tsakiya Ta Zama Makabartar Manufofin Amurka
(last modified Fri, 04 Jan 2019 12:53:55 GMT )
Jan 04, 2019 12:53 UTC
  • Limamin Tehran: Gabas Ta Tsakiya Ta Zama Makabartar Manufofin Amurka

Wanda ya jagoranci Sallar juma'a a Tehran ya bayyana cewa; Gwagwarmayar al'ummar Iran ta sa manufofin Amurka a gabas ta tsakiya suna rushewa

Hujjatul-Islam Muhammad Jawad Haj Ali Akbari ya kuma bayyana yadda al'ummar Iran ta yi gwgawarmaya da jajurcewa akan tafarkinta ba tare da mika wuya ga masu girman kai ba

Har ila yau Limamin na Tehran ya yi ishara da ranar 22 ga watan 10 na Hijira shamshiyya wacce ita ce ranar cin juyin juya halin musulunci, sannan ya kara da cewa; al'ummar Iran ba su da wata rana ta kasa wacce ta kai ta. 

Bugu da kari limamin ya kuma bayyana cewa; a cikin shekaru 40 na cin nasarar juyin musulunci babu wani makirci wanda makiya ba su kitsawa Iran, sai dai wannan bai hana Iran din ci gaba ba ta fuskoki da dama