An Zargi Saudiyya Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Hudaidah
Kakakin sojan kasar Yemen ya bayyana jiya juma'a cewa; Kawancen yakin Saudiyyar yana ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Hudaidah
Kakakin sojojin na Yemen Yahya al-sari'i, ya kara da cewa; A cikin sa'o'i 48 da suka gabata Jiragen yakin Saudiyyar sun keta yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Hudaidah har sau 89
Bangarorin da suke yaki da juna a kasar Yemen sun kulla yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a yankin Hudaidah a cikin watan Disamba na 2018 a kasar Sweeden. Sai dai tun daga wancan lokacin Saudiyyar da 'yan korenta a cikin kasar Yemen suna ci gaba da keta yarjejeniyar
Tun a 2015 ne dai Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa su ka shelanta yaki akan kasar Yemen, wanda har yanzu yake ci gaba. A bisa rahoton Majalisar Dinkin Duniya, adadin mutanen da aka kashe sun kai 13,000 yayin da wasu dubun dubata suka jikkata